Lafiya

Cutar Zika ta dade a duniya kafin ta bayyana

Cutar Zika na sa ana haihuwar jarirai da karamin kai
Cutar Zika na sa ana haihuwar jarirai da karamin kai REUTERS/Paulo Whitaker/File Photo

Wasu masana da ke binciken kiwon lafiya sun ce cutar Zika da ke sanadin haihuwan yara da nakasa a jikinsu ta kwashe sama da shekaru 50 a duniya kafin ta fara bayyana a 2013.

Talla

Rahotan binciken da aka wallafa a Mujallar lafiya ta Amurka ya yi karin haske kan yadda cutar da a can baya ba ta da wani illa ta rikide ta zama barazana ga duniya.

Ana kamuwa da cutar Zika ne daga cizon sauro, kuma ta fi yin illa ga mata ma su juna biyu. Sannan ana kamuwa da cutar ta hanyar jima’I tsakanin wanda sauron Zika ya ciza.

Masanan sun dangata rikidewar cutar da barkewar ta a Polynesia da ke kasar Faransa a shekarar 2013.

A shekarar 2015 cutar ta zama annoba a Brazil bayan kashe mutane 84.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana cutar a matsayin annoba a 2015 bayan ta kasha mutane sama da 80 a Brazil da kuma haifar jarirai da karamin kai.

Yanzu cutar ta bazu zuwa kasashe 84 a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.