Norway

An bai wa kungiyar ICAN kyautar yabon zaman lafiya ta Nobel

Masu fafutukar kawo karshen makaman nukiliya a duniya
Masu fafutukar kawo karshen makaman nukiliya a duniya Britta Pedersen / dpa / AFP

An bayar da kyautar yabo ta zaman lafiya a duniya ga kungiyar nan mai fafutukar ganin an kawo karshen amfani da makaman nukiliya a duniya ICAN., sakamakon namjin kokarin da kungiyar ke yin a ganin an kwance wa duniya damarar makaman nukiliya.

Talla

Kwamitin da ke duba cancanta kafin bayar da kyautar yabon ta Nobel, shi ne ya sanar da bai wa kungiyar wannan tukuici a yau juma’a a birnin Oslo, lura da tsawon shekarun da ICAN ta share tana fafutuka a wannan fage.

Kwamitin da ke bayar da kyautar ta Nobel, ya bi diddigin gwagwarmayar da kungiyoyi suka yi a tsawon shekaru 70 da suka biyo bayan harin da Amurka ta kai makaman nukiliya kan biranen Hiroshama da Nagasaki na kasar Japan, domin duba cancantar wannan kungiya.

Shugabar kwamitin bayar da kyautar Berit Reiss-Andersen ‘yar kasar Norway, ta ce an bayar da kyautar ne domin janyo hankulin duniya dangane da karuwar barazanar yin kerawa ko kuma amfani da irin wannan makami a wannan zamani.

A shekara ta 2007 ne aka kafa kungiyar mai suna ICAN lokacin taron kasashen duniya domin hana bazuwar makaman nukiliya da aka gudanar a birnin Vienna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.