Najeriya- MDD

Najeriya ce kasa ta 27 da ke da 'yan mata marasa ilimi

Rikicin Boko Haram ya haifar da cikas wajen ilmantar da kananan yara mata a yankin arewa maso gabashin Najeriya
Rikicin Boko Haram ya haifar da cikas wajen ilmantar da kananan yara mata a yankin arewa maso gabashin Najeriya UNHCR/K.Mahoney

A yayin da ake bikin ranar kananan yara mata da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a yau, wani sabon rahoto ya nuna cewa, Najeriya ce kasa ta 27 da ‘yan mata ke fuskantar koma-baya wajen samun ilimi a duniya.

Talla

Rahoton da kungiyar ONE CAMPAING ta fitar, ya bayyana Sudan ta Kudu a matsayin kasar da ‘yan mata suka fi fuskantar matsalar samun ilimi, in da Jamhuriyar Tsakiyar Afrika da Nijar ke a matsayi na biyu da na uku.

Rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya ya haifar da gagarumar matsala dangane da fafutukar ilmantar da kananan yara mata bayan kungiyar ta ce, ilimin boko haram ne.

A shekarar 2014, kungiyar Boko Haram ta sace ‘yan matan makarantar Chibok 276 a jihar Borno, amma an yi nasarar ceto wasu daga cikinsu.

Kungiyar ta kuma lalata makarantu fiye da 1,000 a yankin, yayin da kuma aka rufe makarantu 1,500 kamar yadda rahoton ya nuna.

Rahoton ya ce, kashi 52 na ‘yan mata a yankin arewa maso gabashin Najeriya ba sa zuwa makarantar boko, lamarin da ya sha ban-ban da takwarorinsu na yanki kudancin kasar, in da ake da kashi 5 na matan da ke zaune ba tare da neman ilimi ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta ware wannan ranar ce don nazari da kuma bayyana matsalolin da yara mata ke fuskanta da zimmar magance su.

Bikin na bana zai mayar da hankali ne kan matsalolin da ‘yan matan ke fama da su musamman wadanda ke rayuwa a yankunan da ake fama da tashin hankali.

Akan yi amfani da wannan biki domin janyo hankalin shugabanni da iyaye kan rawar da ya dace su taka domin ganin ba a dakilewa yaran hanyoyin cimma burinsu a rayuwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.