Amurka

An zargi Weinstein da yin lalata da 'yan fim

Fitaccen mai shirye fina-finai a masana’antar Hollywood ta Amurka, Harvey Weinstein
Fitaccen mai shirye fina-finai a masana’antar Hollywood ta Amurka, Harvey Weinstein REUTERS/Mike Blake

Fitaccen mai shirye fina-finai a masana’antar Hollywood ta Amurka, Harvey Weinstein na ci gaba da shan suka sakamakon zarginsa da wasu mata suka yi, in da suka bayyana cewa sai ya yi lalata da su kafin ba su damar haskawa a fina-finai.

Talla

Fitattun ‘yan siyasa da suka hada da tsohon shugaban kasar Barack Obama da Uwargida Hilary Clinton na cikin wadanda suka caccaki Weinstein bisa wannan aika-aika.

Mata da dama ne ke zargin Harvey Weinstein, fitacce a masana’antar Hollywood da tirsasa musu yin lalata da shi kafin ba su damar haskawa a fina-finai.

Matan da suka zargi Weinstein mai shekaru 65 da yin lalata da su sun hada da Fitacciyar Jaruma Angelina Jolie da Rosanna Arquette da Gwyneth Paltrow da kuma wata jaruma Bafaranshiya, Judith Godreche.

Angelina Jolie, daya daga cikin jaruman masana'antar Hollywood da ke zargin Weinstein da cin zarafinsu.
Angelina Jolie, daya daga cikin jaruman masana'antar Hollywood da ke zargin Weinstein da cin zarafinsu. AFP PHOTO/GIANLUIGI GUERCIA

Da dama daga cikin matan sun ce, da farko sun yi shiru da bakinsu kan wannan lamari saboda fargabar cewa, Weinstein na iya korar su daga Hollywood.

Tuni dai kamfaninsa ya raba gari da shi saboda wannan badakala da ke ci gaba da daukan hankulan Amurkawa, yayin da ita ma matarsa, Georgina Chapman ta bayyana shirinta na rabuwa da shi.

Sai dai Mr. Weinsten ya musanta wannan zargi da ake yi ma sa.

Ana yawan zargin masu fada a ji a masana’antun fina-finai na kasashen duniya da yin amfani da karfin ikonsu wajen tirsasa wa mata yin lalata da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI