Portugal

Gobarar daji ta hallaka mutane a Portugal

Jami'an kashe gobara na kokarin kashe wutar dajin da ta tashi a Portugal
Jami'an kashe gobara na kokarin kashe wutar dajin da ta tashi a Portugal Spanish Defence Ministry/UME/Luismi Ortiz

Mutane da dama suka rasa rayukansu sakamakon gobarar daji da aka samu a arewacin da tsakiyar Portugal a sa’o’I 24 da suka gabata.Firiainistan Kasar, Antonio Costa, ya kafa dokar ta baci a kasar tare da tura sama da masu kashe gobara dubu 4 domin aikin ceto.

Talla

Mutane kusan 30 hukumar kare rayukan fararen hula a kasar ta tabbatar da mutuwarsu a ibtila’in da ke zuwa watanni 4 bayan mutuwar mutane 64 da jikkatar wasu 250 a irin wannan gobara da ta kasance mafi muni a tarihin kasar.

Mutanen Portugal na yada hotunan wutar dajin a kasar

Kakakin hukumar Patricia Gasper ta ce, an samu tashin gobara sama da 500 a ranar Lahadin da ta gabata, wanda ke da alaka da sauyin yanayi a wannan lokaci da ya haifar da fari, wanda kuma tun farkon wannan shekara ake fama.

Wata mazauniyar garin Penacova da ke zantawa da gidan tabijin RTP na kasar ta ce, sun shiga rudani da tashin hankali gani yadda gobara ke tashi a ko’ina cikin kasar babu kakautawa.

Akwai ‘yan uwan juna maza biyu da suka rasa rayukansu a kokarin aikin ceto a cewar mazauna yankin.

Rahotanni sun ce, an arewa maso yammacin yankin Galicia da ke Spain an samu irin wanan tashin gobara da ya yi sanadi rayuka 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.