Isa ga babban shafi
FOA

Yau ake bikin ranar samar da abinci ta duniya

Hukumar abinci ta duniya ta ce hadin-kai da taimakon juna zai taimaka wajen kawar da yunwa a duniya
Hukumar abinci ta duniya ta ce hadin-kai da taimakon juna zai taimaka wajen kawar da yunwa a duniya WFP
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
1 Minti

Yau ake bikin ranar samar da abinci ta duniya wadda Majalisar Dinkin Duniya ke shiryawa kowacce shekara a karkashin hukumar samar da abinci ta duniya.

Talla

Bikin na yau mai taken sauya makomar gobe, zai mayar da hankali ne kan samar da abinci da kuma raya yankunan karkara domin hana mazauna yankin kwarara birane.

Darakta Janar na hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin duniya Jose Graziano da Silva zai jagoranci wani biki da za’ayi a Geneva wanda zai samu halartar Fafaroma Francis da ministocin kula da ayyukan noma da ke halartar wani taron kasashen G-7.

Hukumar samar da abinci ta Duniya ta ce yake-yake na ta'azara yunwa da hijira

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.