Rikicin Rohingya a Myanmar

Dubban mutanen Rohingya sun nemi mafaka a Bangladesh saboda tashin hali a jihar Rakhine da ke Myanmar
Chanzawa ranar: 24/10/2017 - 13:07

Kusan 'yan kabilar Rohingya miliyan daya ne suka tsere zuwa Bangladesh sakamakon tashin hankalin da ya cika da su a jihar Rakhine da ke Myanmar.  Majalisar Dinkin Duniya ta zargi sojojin Myanmar da kokarin share wata al'umma dag doran kasa ganin irin mummunar kisan da suka yi a Rakhine. Rikicin na baya-bayan nan ya samo asali ne bayan 'yan tawayen Rohingya sun kai hari kan wani ofishin jami'an 'yan sandan kasar a cikin wata Agustan da ya gabata.