Argentina

Masu ra'ayin jarin hujja sun yi nasara a zaben Argentina

Mauricio Macri da kuma gwamnan birnin Buenos Aires Maria Eugenia Vidal na murnar nasarar da suka sama a zaben 22 ga watan oktoban 2017.
Mauricio Macri da kuma gwamnan birnin Buenos Aires Maria Eugenia Vidal na murnar nasarar da suka sama a zaben 22 ga watan oktoban 2017. REUTERS/Marcos Brindicc

Dan takarar jam’iyyar masu ra’ayin jari hujja Mauricio Macri, ya yi nasara a zaben da aka gudanar jiyar lahadi Argentina.

Talla

Jam’iyyarsa Cambiemos ta samu 41% na kuri’un da aka kada a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar, inda kai-tsaye ta lashe kujeru a larduna 13 daga cikin 24 da ake da su a kasar ta Argentina.

 

Har ila yau tsohuwar shugabar kasar Cristina Kirchner ta yi nasarar lashe kujerar shiga zauren majalisar dattawan kasar a zaben na jiiya domin wakilatar Buenos Aires fadar gwamnatin kasar da akalla kashi 37%.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI