'Rashin hukunta masu kashe 'yan Jaridu na haifar da tashin hankali'

Aikin jarida na fuskantar barazana a wasu kasashen Duniya
Aikin jarida na fuskantar barazana a wasu kasashen Duniya Ozan Kose/AFP

Kungiyar da ke kare hakkokin 'yan Jaridu ta Duniya ta ce rashin hukunta masu kashe 'yan Jaridu na haifar da tashin hankali da kuma daukar fansar da kan dauki sama da shekaru 10.

Talla

Kungiyar ta yi wannan bayani ne a rahotan ta na shekara-shekara da ta fitar.

Rahotan kungiyar da ke kare 'yan Jaridu karo na 10 ya bayyana kasashen da aka fi hallaka 'yan Jaridu lokacin gudanar da ayyukan su ba tare da an hukunta kowa ba.

Kasar Somalia ita ce kasar da lamarin yafi kamari cikin kasashe 7 da akafi samun matsalar a duniya.

Sauran sun hada da India da Iraqi da Mexico da Pakistan da Philippines da kuma Rasha.

Elizabeth Witchel, wadda ta jagorancin wallafa rahotan ta ce irin wannan na hana jama’a samun bayanan da suka dace.

Witchel ta ce duk lokacin da aka kashe dan jarida guda, matakin kan razana sauran 'yan Jaridu da kuma yi musu barazana wajen gudanar da aikin su.

Rahotan ya ce a wannan shekara ta 2017 an kashe 'yan Jaridu a kasashe 12.

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wani shirin daukar mataki domin kare lafiyar 'yan Jaridu wanda yanzu haka ya shiga shekaru na 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI