Isa ga babban shafi
Amurka

Donald Trump ya gargadi masu neman rena Amurka

Donald Trump Shugaban Amurka a Yokota dake kasar Japan
Donald Trump Shugaban Amurka a Yokota dake kasar Japan ©. REUTERS/Jonathan Ernst
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 min

A Japan Shugaba Trump ya yi gargadi mai zafi ga wadanda ke kokarin rena matsayin kasar sa, yana mai cewa duk wanda ya kuskura ya aikata hakan, to ko shakka babu zai girbi mummunan sakamako.

Talla

Trump dake gabatar da jawabi zuwa ga dakarun Amurka na yankin Yokota a kasar Japan, bai ambaci sunan wata kasa ba a jawabi nasa, to amma hakan na a matsayin sako ga mahukuntan kasar Koriya ta Arewa.

Shugaba Donald Trump ya tabbatar da cewa Amurka zata kare kan ta tareda yi amfani da dukkanin karfin da ta ke da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.