Asiya

Antonio Guterres ya bukaci yan Rohingya su koma gida

Aung San Suu Kyi jagorar gwamnatin Myanmar
Aung San Suu Kyi jagorar gwamnatin Myanmar REUTERS/Erik De Castro

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci gwamnatin Myanmar da ta bar yan kabilar Rohingya Musulmi da suka gudu suka bar kasar komawa gidajen su, a ci gaba da matsin lambar da ake yiwa gwamnatin kasar.

Talla

Guterres ya yi ganawa da jagorar gwamnatin Myanmar, Aung San Suu Kyi a Manila, ya shaida mata bukatar ganin an baiwa jami’an sa damar kai kayan agaji ga mabukata daga cikin wadanda tashin hankalin ya ritsa da su.

Shima Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya gana da Suu Kyi, amma babu Karin bayani kan abinda suka tattauna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.