Bosnia

Mladic zai sha daurin rai da rai

Ratko Mladic
Ratko Mladic REUTERS/Martin Meissner

Kotun duniya da ke Hague ta yanke wa tsohon Kwamandan Sojojin Serbia, Ratko Mladic hukuncin daurin rai da rai bisa samun sa da aikata laifukan yaki da suka hada da kisan kiyashi a lokacin rikicin Bosnia shekaru 22 da suka gabata.

Talla

Shari’ar Ratko Mladic da ake kira 'The Butcher of Bosnia' ita ce ta karshe a gaban alkalan da aka wakilta don yanke hukunci kan rikicin wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimani dubu 100 tare da raba miliyan 2.2 da muhallansu.

Har yanzu akwai mutane dubu 7 da suka bace a sanadiyar yakin.

Alphons Orie shi ne alkalin da ya jagoranci yanke hukuncin, kuma ya ce laifukan da Mladic ya aikata an sanya su a jerin mayan munanan laifukan da al’ummar duniya ta sani, kuma sun hada da kisan kare dangi da share wata al’umma daga doran kasa, abin da ake kallo a matsayin laifukan yaki.

Mr. Mladic mai shekaru 74 dai shi ne Kwandan da ya jagoranci dakaru a lokacin kisan kiyashin da aka yi wa ya Musulman Bosnia a wancan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.