Amurka

Amurka ta janye batun kulle Ofishin Falasdinu

Yanzu haka dai Amurkan ta bai wa Ofishin na Falasdinu da ke birnin Washington wa'adin kwana 90 kafin ta sanar da kulle shi.
Yanzu haka dai Amurkan ta bai wa Ofishin na Falasdinu da ke birnin Washington wa'adin kwana 90 kafin ta sanar da kulle shi. Reuters

Amurka ta janye sanarwar baya bayan nan da ta fitar na neman kulle ofishin Palasdinu da ke birnin Washington DC, bayan barazanar da Palasdine ta yi na kawo karshen tattaunawar da ta ke da Amurka kan zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya.

Talla

A makon daya gabata ne, Amurka ta yi ikirarin kulle ofishin na Palastine a matsayin martini kan yunkurin Palastine na shigar da karar wasu manyan jami’an Isra’ila kan zargin ci musu iyaka da kuma tayar da zaune tsaye.

Sai dai kuma wata sanarwa da gwamnatin Amurkan ta fitar a yammacin jiya, ta ce ta amince da ci gaba da kasancewar Ofishin a Washington har zuwa nan da kwanaki 90 masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.