Ibrahim Yacouba kan taron Abidjan

Sauti 03:34
Shugabannin kasashen Afrika da Turai na taro a Abidjan
Shugabannin kasashen Afrika da Turai na taro a Abidjan ISSOUF SANOGO / AFP

A yau laraba ake fara taron koli karo na biyar da zai hada shugabannin kasashen Turai da na Afrika a birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire.Wakilai sama da dubu biyar daga kasashe da kuma kungiyoyi akalla 80 ne ke halartar wannan taro da zai mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi matasa a wannan zamani. Abdoulkarim Ibrahim Shikal wanda yanzu haka ke can birnin na Abidjan, ya zanta da ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar Ibrahim Yacouba dangane da abubuwan da taron zai mayar da hankali a kai.