Yemen

Sabon rikici ya barke tsakanin 'Yan tawayen Houthi

Wasu daga cikin mayakan Houthi kenan bayan yanke yarjejeniyar kwancen da ke tsakaninsu da mayakan da ke biyayya ga tsohon shugaban kasar tare da ayyana yaki tsakaninsu.
Wasu daga cikin mayakan Houthi kenan bayan yanke yarjejeniyar kwancen da ke tsakaninsu da mayakan da ke biyayya ga tsohon shugaban kasar tare da ayyana yaki tsakaninsu. REUTERS/Naif Rahma

Sabon yaki ya kara kaurewa a Sanaa babban birnin kasar Yemen bayan da ‘yan tawayen Houthi suka kawo karshen yarjejeniyar kawancen shekaru 3 da ke tsakaninsu da mayakan da ke biyayya ga tsohon shugaban kasar Ali Abdallah Saleh.

Talla

Yanzu haka dai mayakan na Houthi sun watsu a sassan birnin na Sanaa inda su ke kulle shagunan kasuwanci da makarantun tare da ikirarin cewa an fara sabon yaki tsakaninsu da sojin na Shugaba Ali Saleh Abdallah.

A makon da ya gabata ne 'Yan tawayen na Houthi su ka zargi tsohon shugaban kasar Ali Abdallah Saleh da yunkurin yi musu zagon kasa tare da hada hannu da mayakan da Saudiyya ke wa jagorancin don yakar mayakan na Houthi.

A bangare guda kuma mayakan da ke biyayya ga tsohon shugaban sun musanta ikirarin da ‘yan tawayen Houthi suka yi na cewa sun kwace iko da Sanaa babban birnin kasar.

A safiyar yau Lahadi ne dai ‘Yan tawayen na Houthi suka sanar da cewa sun kwace iko da manyan biranen kasar 3 da suka hadar da Sanaa da birnin Dhamar dama wasu sassan yammacin Sanaa.

Tun ranar Laraba ne dai wani sabon rikici ya barke tsakanin ‘yan tawayen da mayakan da ke biyayya ga Shugaba Ali Abdallah Saleh wanda ake kyautata zaton yayi sanadin mutuwar fiye da Mutum 40.

Duk da cewa an samu shawo kan rikicin cikin daren jiya Asabar amma wasu mazauna birnin sun ce rikicin ya dawo sabo a yau Lahadi inda yanzu haka suke zaune cikin tsoro da razani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.