France

Yankin Caledonia zai kada kuri'ar yiwuwar ballewa daga Faransa

Yankin Caledonia na daga cikin yankunan da Faransa ke takama da su musamman ta fuskar yawon bude ido.
Yankin Caledonia na daga cikin yankunan da Faransa ke takama da su musamman ta fuskar yawon bude ido. Wikimedia

Kasa da shekara daya kafin gudanar da kuri’ar raba gardama domin samun ‘yancin-kan yankin Caledonia daga Faransa, yanzu haka firaministan Faransa Edouard Philippe na ziyarar aiki a yankin.

Talla

A watan nuwambar shekara mai zuwa ne al’ummar yankin na Caledonia za su kada kuri’ar raba gardama domin bayyana matsayinsu na samun ‘yanci ko kuma ci gaba da kasancewa karkashin kulawar kasar Faransa.

An share tsawon shekaru 30 ana tsara yadda za a gudanar da wannan zabe, wanda zai fayyace makomar yanki da ke karkashin kulawar Faransa tun a shekarar 1853, lokacin da Sarki Napoleon na uku ya kwace shi daga hannun Birtaniya.

Caledonia, yanki ne da ke da yawan al’umma sama da dubu 280, sannan yake da matukar muhimmanci ga Faransa musamman ta fannin yawon bude ido akan tekun India.

Bayan share tsawon shekaru karkashin mulkin mallakar Faransa, mazauna yankin sun fara kiraye-kiraye domin sun samun ‘yancin kai ne a farkon shekarun 1980, to sai dai gwagwarmayar ta kara zafafa ne a lokacin da masu bore a yankin suka kashe jami’in tsaron Faransa daya sannan suka yi garkuwa da wasu 27 a 1988.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI