Amurka

Amurka ta janye daga yarjejeniyar karbar baki

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/James Lawler Duggan

Amurka ta janye daga yarjejeniyar tinkarar matsalar ‘yan gudun hijira da ‘yan cirani ta Majalisar Dinkin Duniya. A bara ne kasashe 193, mambobi a Majalisar Dinkin Duniya suka amince da wannan yarjejeniya a birnin New York.

Talla

Ofishin Jakadancin Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ya shaida wa Babban Magatakardar Majalisar cewa, kasar ta kawo karshen rawar da ta ke takawa a yarjejeniyar tinkarar matsalolin ‘yan gudun hijira da ‘yan cirani.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnety International ta soki matakin da Amurka ta dauka a dai dai lokacin da duniya ke fama da matsancin matsalar ‘yan gudun hijira.

Yarjejeniyar ta lashi takobin tabbatar da ‘yancin ‘yan gudun hijira ta hanyar samar mu su da wuraren zama tare da ba su ilimin boko da kuma ayyukan yi.

Sai dai Amurka ta ce, yarjejeniyar na kunshe da wasu abubuwa da dama da suka saba da tasre-tasren kasar game da shige da fice da kuma karbar ‘yan gudun hijira, a dalilin haka ne shugaba Donald Trump ya yanke shawarar janye kasar daga wannan yarjejeniya.

Amurka ta janye daga yarjejeniyar karbar baki

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley ta ce, kasar za ta ci gaba da taimaka wa ‘yan gudun hijira da ‘yan cirani a sassan duniya amma ta ce, Amurkawa ne kadai ke da hurumin samar wa kasar tsare-tsaren shige da fice da kuma kula da kan iyakoki.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta nuna damuwa kan sabon matakin na Amurka.

Ba a karon farko kenan ba da shugaba Donald Trump ke janye Amurka daga makamanciyar wannan yarjejeniya, domin ko a ‘yan kwanakin da suka gabata sai da ya janye kasar daga yarjejeniyar dumamar yanayi da aka cimma a birnin Paris na Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.