Girka-Turkiya

Erdogan ya kai ziyara mai cike da tarihi a Girka

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan REUTERS/Murad Sezer

Shugaba Racep Tayyip Erdogan ya fara ziyarar aiki irinta ta farko da wani shugaban Turkiyya ya kai a kasar Girka cikin shekaru 65, ziyarar da ake fatan za ta taimaka domin wareware sabanin iyaka a tsakaninsu.

Talla

Kafin tashinsa zuwa Girka domin fara wannan ziyara, a wani jawabi da ya gabatar gidan talabijin, shugaba Racep Tayyip Erdogan ya ce, yana fatan ziyarar za ta taimaka wajen inganta alaka tsakanin kasashen biyu, tare da yiyuwar sake bitar wata yarjejeniya da suka kulla tun a 1923 wadda ta fayyace iyakokinsu.

Dangantaka tsakanin Girka da Turkiyya wadanda dukkaninsu bambobi ne a Kungiyar Tsaro ta NATO ta kasance mai tsami a tsawon shekaru, to sai dai ta kara tabarbarewa ne a 1996 in da sauran kiris kasashen su gwabza yaki sakamakon takaddama kan mallakar wasu tsibirai.

Har ila yau kasashen biyu na taka muhimmiyar rawa a siyarar Cyprus, kasar da ke a matsayin gungu biyu, daya da ke samun goyon bayan Girka, yayin da Turkiyya ke mara wa daya bangare baya.

To sai dai yayin da kasashen biyu ke kokarin ganin sun warware sabani dangane da mallakar iyaka da kuma samun iko da wasu tsibirai, sai Girka ta bai wa wasu manyan kwamandojin sojin Turkiyya da ake zargi da yunkurin kifar da gwamnatin Erdogan mafakar siyasa a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.