Isra'ila

Matakin Trump ya haddasa tarzoma a birnin Kudus

Tarzoma ta barke a yankin yamma ga Kogin Jordan bayan shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila. Rahotanni na cewa, jami’an tsaron Isra’ila sun yi amfani da barkonon-tsohuwa da kuma harsashin roba, abin da ya raunata Falasdinawa kusan 20.

Jami'an tsaron Isra'ila na harba harsashan roba a tsakiyar Falasdinawa da ke zanga-zangar adawa da matakin Trump na ayyana Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila
Jami'an tsaron Isra'ila na harba harsashan roba a tsakiyar Falasdinawa da ke zanga-zangar adawa da matakin Trump na ayyana Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila REUTERS/Mussa Qawasma
Talla

Matakin shugaba Tump ya janyo masa caccaka daga kasashen duniya da suka hada da aminan Amurka.

Ko a baya-bayan nan kasashen da suka gargadi Trump sun hada da Turkiya da Rasha Faransa da Kungiyar Kasashen Turai, yayin da a nahiyar Afrika Morocco da Senegal suma suka bayyana damuwarsu.

Hoton tarzoma a yankin yamma ga kogin Jordan a wannan Alhamis
A lokacin da Falasdinawa ke taho mu gama da jami'an tsaron Isra'ila REUTERS/Mohamad Torokman

Matakin na Trump dai ya haifar da fargabar zubar da jini da kuma tsananta rashin zaman lafiya a Falasdinu, yayin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bukaci sauran kasashen duniya da su bi sahun Trump a maimakon caccakarsa.

Muryar Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ka matakin Trump

Tuni mahukuntan Falasdinu suka fusata , in da suke cewa ba za su amince da yunkurin Trump ba.

Shugaban Falasdinu Mahmud Abbas ya ce, Kudus zai ci gaba da kasancewa babban birnin Falasdinu har abada.

Muryar shugaban Falasdinu Mahmud Abbas kan matakin Trump

Nan da ‘yan kwanaki masu zuwa ne ake saran Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Larabawa za su gudanar da taro don tattaunawa kan wannan mataki na shugaba Trump.

Matakin shugaba Tump ya janyo masa caccaka daga kasashen duniya da suka hada da aminan Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI