Qatar-Faransa

Qatar ta siyi jiragen yaki daga Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani ©KARIM JAAFAR / AFP

Kasar Qatar ta sanar da kulla yarjejeniyar siyan jiragen yaki 12 daga Faransa kan Euro biliyan 1.1 , yayin da ta ke fama da rashin jituwa da kasashen Larabawa da suka yanke hulda da ita a rikicin siyasa mafi girma a yankin Gulf .

Talla

Qatar ta sanar da hakan ne a ziyara aiki da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kai kasar, kazalika yarjejeniyar ta ba ta damar siyan karin jirage 36  nan gaba.

Wannan ciniki na cikin yarjejeniyar 2015 da suka cimma da Faransa na siyansar manyan jiragen 24.

Kazalika Kamfanin Qatar Airways ya sanar da kulla yarjejeniyar Euro biliyan 5 da rabi domin siyan jiragen sama 50 da zabin karin 36 nan gaba.

Kasashen biyu sun kuma kulla yarjejeniyar Euro biliyan 3 da rabi don inganta tashar jirgin kasa a Doha da yanzu haka ake ginawa a shirye-shiryen da ta ke yi na karban bakwancin wasanni cin kofin duniya a shekara ta 2022.

Shugaba Macron da Sarki Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani sun sanya hannu a sabbin kwangilolin da ke zuwa a dai-dai lokacin da dangantaka tsakanin kasar da sauran kasashen yankin Gulf ke tsami.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI