Isra'ila

Birnin Kudus: Kasashen Musulmi sun yi zanga-zanga

Kasashen Musulmi da suka hada da Lebanon da Indonisia da Morocco da Masar sun gudanar da zanga-zanga a karshen mako don nuna adawa ga matakin shugaban Amurka Donald Trump na ayyana Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila.

Wasu daga cikin  mutanen Indonesia da ke zanga-zangar adawa da matakin Trump na ayyana Kudus a matsayi babban birnin Isra'ila
Wasu daga cikin mutanen Indonesia da ke zanga-zangar adawa da matakin Trump na ayyana Kudus a matsayi babban birnin Isra'ila REUTERS/Darren Whiteside
Talla

A yayin gudanar da zanga-zangar a kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Beirut na Lebanon, jami’an tsaro sun yi amfani da barkonon tsohuwa da ruwan zafi don tawatsa masu gangamin adawa da matakin Trump.

Masu zanga-zangar sun yi ta daga tutar Falasdinu da Lebanon tare da rera wakar zambo ga shugaba Trump.

A can kasar Morocco ma, duban mutane ne suka yi irin wannan gangami a birnin Rabat dauke da tutar Falasdinu, in da suka yi tattaki daga dandalin Babel-Had zuwa Majalisar Dokokin Kasar.

Wasu daga cikin allunan da masu gangamin ke rike da su na cewa “ Kudus, birnin Falasdinu ne”.

‘Yan kasuwa da masu rajin kare hakkin bil’adama na cikin masu zanga-zangar ta nuna adawa da matakin Trump.

Har ila yau an gudanar da gangamin a birnin Jakarta na Indonesia a harabar ofishin jakadancin Amuka , in da akasarin masu gangamin ke sanye da fararen jallabiya da hula.

Allunan da suka rike na cewa “ muna tare da Falasdinawa, a yi wa Falasdinu addu’a”.

Masar ma dai ba a bar ta a ba ya ba wajen gudanar da zanga-zangar, yayin da shugaban Turkiya, Recep Tayyip Erdogan ya bayyana Isra’ila a matsayin kasar ‘yan ta’adda wadda kuma ke kashe kananan yara.

Sai dai a nashi martinin, Firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana Turkiya a matsayin wadda ke jefa bama-bamai kan kauyukan Kurdawa da kuma taimakawa ayyukan ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI