israel

Isra'ila za ta mayar da 'yan ciranin Afrika dubu 40 ƙasashensu

Sansanin Holot da ke kan sahara a Isra'ila na daukan 'yan cirani sama da dubu 1
Sansanin Holot da ke kan sahara a Isra'ila na daukan 'yan cirani sama da dubu 1 AFP

Majalisar Dokokin Isra’ila ta amince da matakin ƙuntatawa ‘yan ciranin da ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa’ida ba, abin da zai bai wa gwamnati damar aiwatar da shirinta na mayar da kimanin baƙi dubu 40 zuwa nahiyar Afrika. Gwamnatin ta bayyana Rwanda da Uganda a matsayin ƙasashen da za ta jibge bakin na Afrika.

Talla

Ma’aikatar cikin gidan Israi’ila ta ce, gabanin mayar da ‘yan ciranin Afrika ƙasashensu na asali, za a bai wa baƙin zaɓi guda biyu, ko dai su amince a mayar da su ƙasashen nasu ko kuma a garkame su a gidan yari.

Tuni Majalisar Dokoki Ƙasar ta ƙada ƙuria’r amincewa da tsauraran matakan matsin lamba kan baƙin da suka haɗa da taƙaita mu su samun kuɗaɗe baya ga ƙayyade mu su wuraren zirga-zirga a ƙasar.

Har ila yau za a ɗauki matakai masu tsauri kan kamfanonin da ‘yan ciranin na Afrika ke aiki, yayin da kuma za a rufe sansanin Holot da ke ɗaukan ‘yan cirani dubu 1 da 200 har tsawon watanni uku.

Wannan sansanin da ke kan sahara na matuƙar taimaka wa ‘yan ciranin musamman wadanda ke aiki a kasar.

Amincawar Majalisar Dokokin na zuwa ne bayan wata babbar kotu ta goyi bayan gwamnatin ƙasar kan wannan batu a cikin watan Agusta.

Ƙungiyar kare hakkin bil’adamna ta Amnesty International ta da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya sun soki wannan mataki na Isra’ila.

Akasarin ‘yan Afrika da ke zaune a Isra’ila sun fito ne daga Eritrea da Sudan kuma suna rayuwa ne a wai yanki da ke kusa da Tel Aviv.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI