Faransa

Karancin kudi na barazana ga yarjejeniyar yanayi ta Paris

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ke karbar bakoncin shugabanni daga sassan duniya daban-daban don halartar taron wanda ke da nufin magance matsalar dumamar yanayi a duniya tare da nemo hanyoyin da za a samar da kudaden gudanarwa.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da ke karbar bakoncin shugabanni daga sassan duniya daban-daban don halartar taron wanda ke da nufin magance matsalar dumamar yanayi a duniya tare da nemo hanyoyin da za a samar da kudaden gudanarwa. PHILIPPE WOJAZER / POOL / AFP

Shuwagabanin kasashen duniya da dama ne a yau talata ke gudanar da taro a birnin Paris na Faransa don kara kaimi wajen samar da kudaden da za a yi amfani da su wajen yaki da matsalar dumamar yanayi a duniya.Rashin kudaden gudanarwa dai na zama babbar barazana ga cimma yarjejeniyar a dai dai lokacin da aka cika shekaru biyu cif da kullata.

Talla

A jawabin buda zaman taron na yau da shugabanni da gwamnatocin duniya da dama suka gabatar, Firaminista Frank Bainimarama, da ya shugaban ci babban zaman taron Majalisar Dinkin Duniya kan dumamar yanayi na (COP23), ya ce kalubalen da ke gaban duniya na da girma, kuma dole ne a tanadi kudaden tafiyar da aikin daga gwamnatoci da kuma kamfanoni masu zaman kansu.

Shugaba Emmanuel Macron na Fransa ya bukaci takwarorinsa faransawa da su yi dukkanin abinda ya dace domin cin nasarar wannan kokowa ta kokarin magance matsalar dumamar yanayi a duniya.

A cewar Macron, ya kamata a hada hannu wajen yin dukkanin abinda ya dace wajen ganin an samu nasara a shirin na yaki da dumamar yanayi a duniya baki daya, tare da samar da sauye sauyen da za su canza da fuskar Faransa, wajen dora ta kan jagorancin yaki da dumamar yanayi a duniya.

Tun bayan janyewar shugaban Amurka Donald Trump daga yarjejeniyar ta sauyin yanayi ne Shugaban na Faransa Emmanuel Macron ya kara matsa kaimi wajen ganin an samu dorewarta tare da cimma abin da aka sanya a gaba.

A shekarar 2015 ne dai kasashen duniya ciki har da Amurka karkashin tsohon shugabanta Barrack Obama suka rattaba hannu kan yarjejeniyar yanayin ta birnin Paris mai dogon tarihi amma daga bisani Amurkan ta fice karkashin shugabanta na yanzu Donald Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI