Libya-Bakin-haure

MDD ta bukaci a kwashe 'yan ciranin Afrika a Libya

Wasu 'yan cirain Afrika a Libya
Wasu 'yan cirain Afrika a Libya REUTERS/Hani Amara/File Photo

Majalisar Dinkin Duninya ta bukaci kasashen Afrika da su kwashe kimanin ‘yan ci rani dubu daya da dari uku da suka rage a Libya, bayan bankado badakalar cinikin bayi a kasar.

Talla

A cewar Mr. Volker Turk Mataimakin babban jami'in hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ya zama wajibi a gaggauta kwashe ‘yan ci ranin nan da watan Maris na shekara mai zuwa.

Mr Turk ya ce, da dama daga cikin ‘yan ci ranin waɗanda galibi mata ne da kananan yara na fama da matsanancin rashin lafiya sakamakon halin kuncin da suka shiga ko dai akan hanyarsu ko kuma bayan fadawarsu hannun masu safarar mutane a Libyan.

Mr Turk ya kara da cewa, dole ne a hada hannu don gaggauta kwashe su tare da kai su kasashensu na asali ba tare da fuskantar jinkiri ko kuma kuskuren kai su kasar tasu ba.

A watan da ya gabata ne hukumar ta kwashe wasu ‘yan cirani 25 da suka kunshi maza 6 da mata 15 da kananan yara 4 ‘yan asalin kasashen Habasha da Sudan da kuma Eritrea amma ta kai su Jamhuriyyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.