Duniya

kananan yara kusan 500 ke mutuwea sakamakon taka nakiyoyi

Wani yankin da aka binne nakiyoyin a kasar Iraqi.
Wani yankin da aka binne nakiyoyin a kasar Iraqi. REUTERS/Essam Al-Sudani

Wani rahoton bincike ya bayyana cewa, kananan yara kusan 500 ne suka rasa rayukansu sakamakon taka nakiyoyi a bara.Rahoton ya ce, akala mutanen da suka mutu ta wannan hanyar a 2016 sun kai dubu 8 da 605, wanda shi ne adadi mafi girma da aka gani tun shekarar 1999.

Talla

Rahoton ya ce, an samu wadannan alkaluman ne sakamakon tsanantar yake-yake a kasashen Afghanisatan da Ukraine da Yemen da kuma Libya.

Rahoton ya ambaci Najeriya da Myanmar da Pakistan da India a matsayin kasashen da kungiyoyin masu dauke makamai suka binne nakiyoyin.

Kusan kashi dya cikin uku na wadanda lamarin ya shafa fararen hula ne da suka hada da kananan yara fiye da dubu 1 da suka samu rauni, yayin da kusan 500 daga cikin yaran suka mutu kamar yadda rahoton ya ce.

Rahoton ya bayyana matsalar a matsayin gagaruma yayin da ake fargabar cewa, akwai yiwuwar alkaluman mamatan ma sun zarce haka, lura da cewa an gaza tattarara alkaluma daga wasu kasashen kamar Syria da Iraqi.

A farkon shekarar nan ne, Yarima Harry na Birtaniya ya bukaci kasashen duniya da su kara kaimi wajen kawar da nakiyoyin karkashin kasa nan da shekarar 2025.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.