Amurka

An tsare wasu karnuka kan kashe uwargidan su

'Yan Sanda na tsare da wasu karnuka guda biyu da ake zargi da kashe uwargidan su
'Yan Sanda na tsare da wasu karnuka guda biyu da ake zargi da kashe uwargidan su KIRO7

Rahotanni Daga kasar Amurka sun ce yanzu haka 'Yan Sanda na tsare da wasu karnuka guda biyu da ake zargi da kashe uwargidan su, Bethany Lynn Stephens, mai shekaru 22 a Jihar Virginia.

Talla

Bayanai sun ce Bethany ta saba fita da karnukan suna kewaye, amma a ranar da hadarin ya auku, sai aka ga bata dawo gida ba, abinda ya sa mahaifin ta ya shaidawa 'Yan Sanda da karfe 8 na dare.

Yayin bin sawun inda ta saba bi ne, aka samu gawar ta da kuma karnukan tsaye a kanta, kuma suka hana kowa zuwa kusa da gawar.

'Yan Sanda sun kwashe sa’a guda kafin nasarar kawar da karnukan, inda suka gano yadda irin ta’adin da suka yi wa Bethany a fuskarta da kuma hannayen ta, wadanda likitoci suka ce abinda ya yi sanadiyar mutuwar ta kenan.

Yanzu dai haka ana nazari kan yadda za’a kashe karnukan da ke hannun 'Yan Sanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI