KOREA TA AREWA

Majalisar Dinkin Duniya ta kara sanyawa Korea ta arewa Takunkumai

Daga cikin sabbin takunkuman Majalisar Dinkin Duniyar kan Korea ta arewa har da mayar da tarin jama'arta gida wadanda ke aiki a wasu kasashen matakin da Majalisar ta kira da cewa yana taimakawa Korea samun kudaden shiga.
Daga cikin sabbin takunkuman Majalisar Dinkin Duniyar kan Korea ta arewa har da mayar da tarin jama'arta gida wadanda ke aiki a wasu kasashen matakin da Majalisar ta kira da cewa yana taimakawa Korea samun kudaden shiga. 路透社。

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kara kakabawa Korea ta Arewa sabbin takunkumai ciki har da rage yawan man fetur din da ake shigarwa kasar kasar da shi daga kasashen Duniya.

Talla

Wannan mataki dai ya zo ne a matsayin wani hukunci sakamakon kunnen-uwar-shegu da kasar ke yi game da kiraye-kirayen da ake yi mata na ta dakatar da shirinta na mallakar makaman nukiliya.

A zaman da kwamitin sulhu na majalisar ya gudanar a yau, daukacin mambobinsa sun nuna goyon bayan su ga kudurin sanya karin takunkumin wanda Amurka ta gabatar.

Daga cikin sabbin takunkuman har da mayar da tarin ‘yan Korea ta arewan da ke aiki a kasashen duniya zuwa kasarsu, wanda majalisar ta ce zai taimaka wajen rage kudaden shigar da gwamnatin kasar ke samu.

Sai dai kuma sa'o'i kalilan kafin amincewa da kudurin, Korea ta arewa ta bakin mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajenta, ta bayyana kudurin na Amurka a matsayin abin assha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI