Guatemala

Kasar Guatemala za ta sauya ofishi zuwa Quds

Jimmy Morales Shugaban kasar Guatemala
Jimmy Morales Shugaban kasar Guatemala Captura de pantalla

Kasar Guatelama ta ce za ta dauke ofishin jakadancinta daga Tel Aviv zuwa Quds domin yin koyi da Amurka.Shugaban Amurka ya bayyana cewa kasar na nan kan matakin da ta dau na mayar da birnin Quds babban birnin kasar Isra'ila. 

Talla

Tuni Shugaban kasar Jimmy Morales ya tabbatar wa Benyamin Netanyahu wannan aniya tasa a wata tattaunawa da suka yi ta wayar tarho,kuma Guatemala dai na daya daga cikin kasashe 9 da suka kada kuri’ar goyon bayan Amurka lokacin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zanta kan wannan batu.

Shugaban A murka Donald Trump ya ce matakin ba zai sauya matsayin Amurka na samun kasashe biyu tsakanin Isra'ila da Falasdinu ba idan sun amince a tsakanin su.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Alla-wadai da matakin da shugaba Donald Trump ya dauka, inda ya ke cewa ta hanyar tattaunawa ne kawai za a warware matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.