Za mu bai wa Falasɗinawa ƙwarya-ƙwaryar ƴanci-Isra'ila
Wallafawa ranar:
Ministan haɗin kan yanki na Isra’ila Tzachi Hanegbi, ya ce matakin da shugaban Amurka ya ɗauka na ayyana Ƙudus a matsayin babban birnin Isra’ila ba zai illata shirin samar da ƙasashe biyu ba a yankin.
Hanegbi ya ce Isra’ila na da aniyar bai wa Falasɗinawa ƙwarya-ƙwaryar yancin kai.
Ya kuma ce matakin da Isra’ila ta ɗauka na iƙirarin kame ɗaukacin Ƙudus a matsayin babban birninta zance ne na fatar baki domin bai zama doka ba.
Hanegbi ya faɗi wa manema labaru cewa Falasɗinawa na da ƴancin ci gaba da neman samun mallakin gabashin birnin na Ƙudus a matsayin cibiyarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu