Isra'ila

Isra'ila ta zargi MDD da nuna son kai a duniya

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. REUTERS/Amir Cohen

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya buƙaci majalisar ɗinkin duniya ta dakatar da shirinta na musamman na taimaka wa Falasɗinawa ƴan gudun hijira.

Talla

Ita dai Isra’ila na kallon shirin na majalisar ɗinkin duniya a matsayin nuna son kai tsakanin bangarorin biyu, abinda majalisar ɗinkin duniyar ta musanta.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar daina bai wa falasɗinawa tallafi.

Netanyahu ya ce dole ne a dakatar da wannan tsari na musamman wanda ke taimaka wa Falasɗinawa, kasancewar dukkanin ƴan gudun hijira na samun kulawa ne ƙarƙashin ofishin jami’i mai kula da masu gudun hijira na majalisar.

Ko a watan Yuni, Netanyahu ya ce ya tattauna zancen da jakadar Amurka a majalisar ɗinkin duniya Nikki Haley.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.