Isra'ila

Isra'ila za ta gina gidaje 1,100 a gaɓar yamma

Gine-ginen Yahudawa.
Gine-ginen Yahudawa. REUTERS/Baz Ratner

Ana kallon irin waɗannan gine-gine da Isra'ila ke yi a matsayin waɗanda suka saɓa wa doka, kuma babban ƙalubale ga shirin samar da ƙasashe biyu, kasancewar ana yin su ne a yankin da Falasɗinawa ke iƙirarin mallaka.

Talla

Kwamiti mai lura da gina matsugunai na ma'aikatar tsaron ƙasar Isra'ila ne ya amince da gina gidajen a ranar Laraba.

A cewar wata ƙungiya mai zaman kanta, Peace Now, a ranar Alhamis, ma'aikatar ta riga ta amince da gina gidajen a gaɓar yamma. Kuma wannan ne mataki na baya-baya da Isra'ila ta ɗauka na gina matsugunai a yankin na Falasɗinu.

Jami'in ƙungiyar 'Peace Now' Hagit Ofran ya shaida wa kamfanin dillancin labaru na AFP cewa an kai matakin ƙarshe na amincewa da gidaje 352, yayin da sauran ke a mataki na farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.