Trump ya musanta furta kalaman wulakanta nahiyar Afrika

Shugaban kasar Amurka Donald Trump.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump. REUTERS/Joshua Roberts

Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta yin amfani da Kalaman cin zarafi wajen siffanta nahiyar Afrika da kuma kasar Haiti.

Talla

Sai dai Trump ya jaddada sukar da ya ke yi wa shirin majalisar dattawan kasar, na amincewa da wata dokar shige da fice, da zata tilastawa Amurka karbar ‘yan ci rani daga kasashen da ya ce suna fama da talauci.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyar Tarayyar Afrika, gwamnatin Haiti, da ma sauran kasashe, suka yi tur da kalaman na wulakanci, da suka bayyana su kai tsaye da cewa na nuna wariya ne, wadanda wasu kafofin yada labarai suka nuna Trump din ya furta, a lokacin da ya jagoranci wani taro kan shigi da ficen baki ‘yan ci rani a fadar White House.

Yayin da yake kare kansa a shafinsa na twitter, Trump ya musanta furta kalamai na kamanta ‘yan kasar ta Haiti da kuma al’ummar nahiyar Afrika a matsayin kazamai, a cewarsa ya dai bayyana su ne a matsayin matalauta wadanda gwamnatocinsu basu da alkibla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.