Syria

Matakin Amurka a Syria ya harkuza Turkiya

Matakin Amurka na kafa sabuwar rundunar soji dubu 30 a Syria ya harkuza Turkiya
Matakin Amurka na kafa sabuwar rundunar soji dubu 30 a Syria ya harkuza Turkiya REUTERS/Rodi Said

Rundunar hadaka karkashn jagorancin Amurka da ke yaki a Syria na shirin kafa sabuwar runduna mai kunshe da dakaru dubu 30 don samar da tsaro kan iyakoki, matakin da ya harzuka Turkiya wadda ke zargin Amurka da tallafa wa mayakan Kurdawa.

Talla

Wani babban jami’in gwamnatin Turkiyya ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa, matakin na Amurka na horar da dakarun don samar da sabbin sojin da za su rika samar da tsaro akan iyakokkin Syria abin damuwa ne .

Za a rarraba sabbin dakarun akan iyakokin da ke hannun ‘yan tawayen kasar da kuma yankunan da ke karkashin Kurdawa, da nufin kawo karshen hare-haren da gwamnatin kasar karkashin jagorancin Rasha da Turkiyya da kuma Iran ke kai wa don kakkabe sauran ayyukan ta’addanci.

Rahotanni sun ce, galibin mayakan an tsamo su ne daga ‘yan tawayen Syria, lamarin da ke zama tamkar tufka da warwara kan nasarorin da gwamnatin kasar ke samu na kawo karshen yakin basasar da aka shafe fiye da shekaru 6 ana fama da shi.

A cewar rahotanni za a girke wasu daga cikin dakarun akan iyakar kasar da Turkiyya, sai kuma wasu akan iyakar kasar da Iraqi yayin da wasu kuma za a bar su a gabar ruwan Valley.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI