Isa ga babban shafi
chile

Fafaroma ya nemi afuwa kan badakalar lalata a Chile

Shugaban mabiya darikar katolika Fafaroma Francis
Shugaban mabiya darikar katolika Fafaroma Francis Reuters
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 Minti

Shugaban Darikar Katolika ta Duniya Fafaroma Francis da ke ziyarar kwanaki uku a Chile, ya nemi afuwa game da badakalar lalata da kananan yara da wani limanin cocin Katolika ya aikata, lamarin da ya haifar da cece-kuce a fadin kasar.

Talla

Wannan badakala ta rage karkashin tarbar da Fafaroma Francis ya samu a wannan ziyara a Chile, saboda yadda wasu mutanen kasar ke nuna bacin ransu ganin cewa, Fafaroman ne ya nada limanin da ke kare wanda ake zargi da lalata kananan yaran.

A yayin gabatar da jawabi a fadar gwamnatin kasar, Fafaroma ya ce, ya damu matuka kuma ya ji kunya kan mummunar dabi’ar da wasu limaman coci ke nunawa, yayin da ya yi alkawarin rashin sake aukuwar hakan nan gaba.

A shekarar 2011 ne, Rev. Fernando Karadima na birnin Osorno da ke kudancin Chile, aka same shi da laifin lalata kananan yaran, lamarin da ya kai ga sauke shi daga mukaminsa.

Sai dai wanda ya gaje shi wato Juan Barros na shan suka a kasar bayan ya ce, ba shi da masaniya kan wannan badalaka wadda ta shafi kimar darikar Katolika a Chile.

Kawo yanzu babu cikakken bayani kan ko Fafaroman zai gana da wadanda aka ci zarafin na su a yayin wannan ziyara.

Ana saran Fafaroman zai jagoranci addu’ar da za ta samu halartar kimanin mutane rabin miliyan kafin daga bisani ya ziyarci gidan kaso na mata a birnin Santiago.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.