Turkiya

Erdogan ya sha alwashin ci gaba da farmakar mayakan Kurdawa

Erdogan ya sha alwashin cewa kowanne lokaci daga yanzu za su kaddamar da farmaki kan mayakan na YPG tare da hadin gwiwa ‘yan tawayen Syria.
Erdogan ya sha alwashin cewa kowanne lokaci daga yanzu za su kaddamar da farmaki kan mayakan na YPG tare da hadin gwiwa ‘yan tawayen Syria. Kayhan Ozer/Presidential Palace/Handout via REUTERS

Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya sha alwashin ci gaba da kai hare-hare yankin Afrin na arewacin Syria da ke karkashin ikon mayakan Kurdawa na YPG masu samun goyon bayan Amurka.Kalaman na Erdogan na zuwa ne a dai dai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da tofa albarkacin baki kan hare-haren saman da Turkiyyan ta jagoranta don fatattakar ‘yan tawayen kurdawan daga Afrin.

Talla

A cewar Erdogan, Sauya sunan 'Yan tawayen kurdawan na YPG ba zai sauya matsayinsu daga ‘yan ta’addan da aka sansu a baya ba, don haka zai ci gaba da kai hare-hare ta sama har sai ya tabbatar da murkushe su daga yankin na Afrin.

Haka zalika, Erdogan ya ce, bisa taimakon mayakan sa kai na Syria da Turkiyyar ta jagoranci girkewa a kan iyakokin Syriyar, zai tabbatar da kwace birnin Manbij da ‘yan tawayen na Kurdawa suka kwace a hannun kungiyar ISIL cikin shekarar 2016.

A daren juma’ar makon jiya ne rundunar sojin Turkiyya ta jagoranci kai farmaki ta sama kan mayakan Kurdawa na kungiyar YPG masu samun goyon bayan Amurka, da ke yankin Afrin a Syria, lamarin da ya shafi cibiyoyin ‘yan tawayen 108.

Erdogan ya sha alwashin cewa, kowanne lokaci daga yanzu za su kaddamar da farmaki kan mayakan na YPG tare da hadin gwiwa ‘yan tawayen Syria.

Sai dai cikin sanawar da suka fitar, kakakin Kurdawan na YPG Birusk Hasaka, ya ce fararen hula 6 sun hallaka a hare-haren, yayin da wasu 13 kuma suka jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.