Jamus zata daina cinikin makamai da kasashen da ke yaki a Yemen

Wasu gine-gine da jiragen yakin rundunar sojin da Saudiya ke jagoranta suka kai wa farmaki a Yemen. 6 Janairu, 2018.
Wasu gine-gine da jiragen yakin rundunar sojin da Saudiya ke jagoranta suka kai wa farmaki a Yemen. 6 Janairu, 2018. REUTERS/Naif Rahma

Kakakin gwamnatin Jamus Steffan Seibert, ya ce kasar zata dakatar da saidawa dukkanin kasashen da cikin yakin kasar Yemen makamai.

Talla

Matakin na Jamus zai shafi cinikin makaman tsakaninta da kasar Saudiya, wadda daga tsakiya zuwa karshen shekarar 2017, Saudiyan ta sayi makaman da kudinsu ya kai dala miliyan 550 daga Jamus.

Kungiyar Amnesty International ta yi maraba da matakin na gwamnatin Jamus, tare da kira ga sauran kasashen su dauki irin matakin.

Rahoton wata hukuma mai fafutukar rage yawan cinikin makamai CAAT, ta ce Birtaniya ta saidawa Saudiya makaman da kudinsu ya zarta fan biliyan hudu da dubu dari shida, tun bayan fara yakin na kasar Yemen.

A watan Maris na 2015, Saudiya ta fara jagorantar rundunar sojin kawayenta, inda ta mayar da hankali wajen kai wa ‘yan tawayen Houthi farmaki da jiragen yaki da nufin murkushe mayakan ta kuma mai do da gwamnatin Abd-Rabbu Mansour Hadi da ‘yan tawayen suka hambarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.