Oxfam

Arzikin duniya ya fada hannun tsirarun mutane a bara

Rahoton Oxfam ya ce, ana amfanin da kuzarin manoma wajen habbaka tattalin arzikin tsirarun mawadata a duniya
Rahoton Oxfam ya ce, ana amfanin da kuzarin manoma wajen habbaka tattalin arzikin tsirarun mawadata a duniya AFP PHOTO / OXFAM / IRINA FUHRMANN

Wani rahoto da kungiyar Oxfam ta fitar ya ce, kashi 82 na arzikin duniya da aka tattara a bara ya fada ne a hannun tsirarun mawadata, yayin da rabin talakawan duniya suka gaza samun wani kaso daga cikin arzikin. 

Talla

Rahoton mai taken “ladan aiki, ba na kudi ba” ya nuna yadda kashi daya na masu hannu da shuni a duniya suka ci gajiyar tattalin arzikin duniya a bara, yayin da kimanin talakawa biliyan 3.7 ke ci gaba da yaki da talauci.

Masu hannu da shuni sun samu habbakar arzikinsu da Dala biliyan 762, kudaden da sun isa su kawar da tsananin talauci da ninki bakwai.

Babbar Darektar Kungiar ta Oxfam mai cibiya a Birtaniya, Winnie Byanyima ta ce, alkaluman da suka tattara sun nuna cewa, an samu akasi a tsarin tafiyar da tattalin arzikin duniya.

Byanyima ta ce, an yi amfani da kuzarin talakawa masu aikin samar da tufafi da wayoyin salula da kuma masu noman abinci wajen habbaka tattalin arzikin tsirarun mawadata.

A bara ne dai aka samu karuwar masu hannu da shuni da a taba ganin yawansu ba a tarihin duniya kamar yadda rahoton na Oxfam ya ce, kuma akasarinsu maza ne.

A cewar rahoton kaucewa biyan haraji da danne hakkokin ma’aikata na daga cikin dalilan tazara tsakanin mawadata da talakawa a duniya.

Rahoton na zuwa ne a yayin da aka bude taron tattalin arziki na duniya a birnin Davos na Switzerland a yau Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.