Isa ga babban shafi
Colombia

Gwamnatin Colombia ta sanar da janyewa daga tattaunawa da kungiyar ELN

Shugaban Colombia  Juan Manuel Santos da wasu Shugabanin yan tawayen ELN
Shugaban Colombia Juan Manuel Santos da wasu Shugabanin yan tawayen ELN Presidencia Colombia
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 Minti

Shugaban Colombia Juan Manuel Santo ya bayyana dakatar da tattaunawa da kungiyar yan Tawayen ELN bayan wani kazamin harin da ta kai a karshen mako wanda ya hallaka yan Sanda 7.

Talla

Shugaban ya ce ya dauki matakin ne saboda ganin yadda kungiyar taki mutunta alkawarin da tayi.

Gwamnatin Santos ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya da babbar kungiyar yan tawayen FARC a shekarar 2016 inda ta rikide ta koma Jam’iyyar siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.