Kotun Belgium na tuhumar maharin birnin Paris
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
An tsaurara matakan tsaro a duk fadin kasar Belgium a daidai lokacin da Salah Abdeslam, mutum daya daga cikin maharan birnin Paris a shekara ta 2015 da ya tsira da rayuwarsa ke sake gurfana a gaban kotun birnin Brussels a wannan litinin.
Abdeslam mai shekaru 28 a duniya, da aka dauke shi cikin tsauraran matakan tsaro daga wani gidan kurkuku da ke Faransa zuwa Belgium, ana tuhumar sa da yunkurin kashe jami’an tsaro da kuma mallakar makamai ba a kan ka’ida ba.
Matukar dai aka same shi da laifi, Abdeslam da kuma wanda aka kama su cikin gida daya tare mai suna Sofiane Ayari, za a iya daure su tsawon shekaru 40 kowannensu.
Harin birnin Paris da kungiyar ISIS ta dauki alhakin kaddamarwa a wancan lokaci ya yi sanadiyar mutuwar mutane 130, yayin da masu shigar da kara na Faransa suka yi amanna cewa, Abdeslam ya taka gagarumar rawa a harin amma ya ki bai wa masu bincike hadin kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu