Falasdinu

Falasdinawa 54 sun mutu kafin samun bizar neman magani daga Isra'ila

Gerald Rockenshaub, jami’in Hukumar a Yankin Falasdinu, ya ce akwai mutane fiye da 25,000 da suka bukaci biza daga Israila domin fita daga Gaza.
Gerald Rockenshaub, jami’in Hukumar a Yankin Falasdinu, ya ce akwai mutane fiye da 25,000 da suka bukaci biza daga Israila domin fita daga Gaza. Reuters/路透社

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla Falasdinawa sama da 50 ne suka mutu bara yayain jiran bizar tafiya neman magani daga hukumomin Israila. Wannan ya biyo bayan matakai masu tsauri da Israila ke dauka na takaita zirga zirga Falasdinawa a Yankin.

Talla

Alkaluman da hukumar lafiyar ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar sun ce Falasdinawa 54 suka mutu, lokacin da suke jiran izinin tafiya neman magani daga Israila a bara.

Kungiyoyin kare hakkin Bil Adama sun danganta matsalar da irin matakan da jami’an gwamnati ke dauka wanda ke hana Falasdinawan samun magani.

Falasdinawa mazauna Gaza da Gabar Yamma da Kogin Jordan da Israila ta yiwa kawanya, su kan sha wahala kafin su samu izinin fita daga Yankin domin samun magani.

Hukumar lafiya ta ce babu hanyar samun kula da masu fama da cutar kansa a Gaza, saboda rashin kayan aiki, yayin da Israila ta hana izinin sayo na’urorin zamani domin kula da marasa lafiyar saboda zargin cewar kungiyar Hamas na iya kwace su.

Gerald Rockenshaub, jami’in Hukumar a Yankin Falasdinu, ya ce akwai mutane fiye da 25,000 da suka bukaci biza daga Israila domin fita daga Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.