Isra'ila-Iran

Anyi musayar zafafar kalamai tsakanin Iran da Isra'ila a Munich

Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif, ya yin jawabi gaban komitin tsaro a Munich da ke kasar Jamus
Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif, ya yin jawabi gaban komitin tsaro a Munich da ke kasar Jamus Reuters

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Javad Zarif ya zargi kasar Isra’ila da haddasa fitina a yankin gabas ta tsakiya sakamakon yadda sojojinta ke yawaita kai hare-hare kasashen Syria da Lebanon a baya bayan nan.

Talla

Javad Zarif ya soki Isra’ilar da kakkausan harshe ne, a lokacin da ya gabatar da jawabi gaban taron tsaro, na kasashen duniya da ke gudana a birnin Munich na kasar Jamus.

Kalaman na ministan harkokin wajen Iran, sun zo ne bayan sauka daga fagen gabatar da jawabi da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi.

A nasa jawabin, Netanyahu, ya kamanta gwamnatin kasar Iran da ta Nazi da ta mulki Jamus a zamanin shugabancin Adolf Hitler.

Yayin da ya ke gabatar da jawabi wajen taro kan sha’anin tsaron karo na farko, Firaministan Isra’ila, ya bayyana Iran a matsayin babbar barazana ga zaman lafiyar Duniya. Kan haka ne Netanyahu ya bukaci kasashen Duniya da su kalubalanci gwamnatin ta Iran.

Dangantaka ta kara yin tsami tsakanin Iran da Isra’ila tun ranar 10 ga watan Fabarairu, bayan da sojin Iran suka harbo wani jirgin yakin Isra’ila, a lokacin da yake kan hanyar dawowa daga farmakin da ya kaiwa cibiyoyin sojin Syria da Iran a kasar Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI