Isa ga babban shafi
MDD

Yau ce ranar harshen uwa ta duniya

Ana bikin ranar tattalin harshen uwa don kare wasu harsunan daga bacewa daga doran kasa
Ana bikin ranar tattalin harshen uwa don kare wasu harsunan daga bacewa daga doran kasa DR
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 Minti

Yau ce ranar da Hukumar Ilimi, Kimiya da kuma tattalin Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato Unesco ta kebe domin tattalin harsunan uwa a duniya.

Talla

Yau dai shekaru 20 kenan da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe wannan rana domin kare wasu daga cikin harsunan da ke barazanar bacewa.

Taken bikin na bana shi ne, "harsuna da karkasuwarsa na da muhimmaci wajen samar da ci gaba mai dorewa".

Bikin na zuwa ne bayan Hukumar UNESCO ta gano cewa, akalla harshe guda daga cikin harsunan da ake da su a duniya na bacewa a kusan kowanne mako biyu, lamarin da ke barazana ga yaduwar al’adun gargajiyar wasu al’umomi na duniya.

Wasu alkaluman hukumar sun nuna cewa, akwai sama da harsuna dunb 7 da ake amfani da su  yau da kullum a sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.