Syria

Babu yarjejeniyar tsagaita musayar wuta a Syria- Rasha

Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vassily Nebenzia
Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vassily Nebenzia Drew Angerer/Getty Images/AFP

Rasha ta shaida wa taron Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, babu wata yarjejeniyar tsagaita musayar wuta ta kwanaki 30 a Syria, yayin da ta gabatar da sauyi a kudirin tsarin shigar da kayayyakin agaji da kwashe fararen hula a yankin Ghouta mai fama da hare-haren dakarun gwamnati.

Talla

Kusan makwanni biyu kenan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke kokarin cimma matsaya kan kudirin tsagaita musayar wuta a dai dai lokacin da dakarun gwamnatin kasar ke ci gaba da ragargazar yankin Ghouta da ke hannun ‘yan tawaye.

Jakadan Rasha a Majalisar, Vassily Nebenzia ya ce, kasashen Sweden da Kuwait da suka bukaci kada kuri’a akan kudirin, na da cikakkiyar masaniya kan cewa, babu wata yarjejeniya a kasa game da tsagaita musayar wutar.

Nebenzia ya ce, Kwamitin Sulhun na bukatar cimma yarjejeniya mai yiwuwa amma ba wadda za ta kasance mai tsauri ba ta yadda za a gaza aiwatar da ita.

Tuni kasashen Amurka da Faransa da Birtaniya suka bukaci Kwamitin da ya gaggauta kada kuri’a kan batun.

Sama da mutane 400 ne suka rasa rayukansu a cikin kwanaki biyar sakamakon farmakin sojin gwamnatin Syria a yankin gabashin Ghouta, lamarin da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana tamkar wutar jahannama a doran kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.