Syria

Kwamitin Tsaro ya gaza samar da tsagaita wuta a Syria

Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vassily Nebenzia ranar 22 ga watan Fabarairun 2018.
Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vassily Nebenzia ranar 22 ga watan Fabarairun 2018. REUTERS/Brendan McDermid

Rasha ta shaida wa taron Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, babu wata yarjejeniyar tsagaita musayar wuta  ta kwanaki 30 a Syria, yayin da ta bukaci a aiwatar da gyara ga daftarin kudirin tsarin shigar da kayayyakin agaji da kwashe fararen hula a yankin Ghouta  mai fama da hare-haren dakarun gwamnati.

Talla

Kusan makwanni biyu kenan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke kokarin cimma matsaya kan kudirin tsagaita wuta a daidai lokacin da dakarun gwamnatin kasar  ke ci gaba da ragargazar yankin Ghouta da ke hannun ‘yan tawaye.

Jakadan Rasha a Majalisar, Vassily Nebenzia ya ce, kasashen Sweden da Kuwait da suka bukaci kada kuri’a a kan kudirin, na da cikakkiyar masaniyar cewa, babu wata yarjejeniya a kasa game da haka.

Nebenzia ya ce,  Kwamitin Sulhun na bukatar cimma yarjejeniya mai yiwuwa amma ba wadda za ta kasance mai tsauri har ma a gaza aiwatar da ita.

Tuni kasashen  Amurka, Faransa da Birtaniya  suka bukaci  Kwamitin da ya  gaggauta kada kuri’a kan batun.

Sama da mutane 400 ne suka rasa rayukansu a cikin kwanaki biyar sakamakon  farmakin sojin gwamnatin Syria a yankin gabashin Ghouta, lamarin da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana tamkar wutar jahannama a doran kasa.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.