Amurka- Iran

Amurka za ta dau mataki kan Iran game da rikicin Yemen

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniyar Nikki Haley, ta ce duk da kin amincewar majalisar wajen daukar matakai kan Iran, Amurkan a radin kanta za ta dauki tsauraran matakai.
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniyar Nikki Haley, ta ce duk da kin amincewar majalisar wajen daukar matakai kan Iran, Amurkan a radin kanta za ta dauki tsauraran matakai. REUTERS/Lucas Jackson

Amurka ta yi barazanar daukar matakai na gaban kan ta a kan Iran, bayan da Rasha ta hau kujerar na ki don hana tabbatar da wani kudurin MDD da ke neman daukar mataki akan Iran saboda rawar da take takawa a rikicin Yemen,

Talla

Jakadiyar Amurka a MDD Nikki Haley, ta ce matukar dai Rasha ta cigaba da bai wa Iran kariya a gaban Kwamitin Tsaro, ita kuwa Amurka da kawayenta za su dauki na su matakan a wajen Majalisar ta Dinkin Duniya.

Iran dai na taka muhimmiyar rawa wajen bayar da gudunmawa ga 'Yan tawayen Yemen a dai dai lokacin da hadakar kawance na Sojin Saudiyya da ke samun goyon bayan Amurka ke yakar 'Yan tawayen.

Ko a baya-bayan nan Saudiyya ta gano wasu makamai da 'yan tawayen ke amfani da su wanda ta ke da yakinin cewa Iran ce ta taimaka musu da makaman ko da ya ke dai a lokuta da dama Iran din na musanta batun.

Haka zalika duk da kokarin da Amuka ke yi wajen ganin Majalisar Dinkin Duniya ta dauki mataki kan Iran din na ta shi a tutar babu, la'akari da yadda Rasha ke yin uwa da makarbiya wajen hana daukar matakan.

Amurkan dai ta ce za ta dauki tsauraran matakai na radin kan ta a wajen zauren Majalisar Dinkin Duniyar kan yadda ta ke ci gaba da tallafawa 'yan tawayen na Yemen.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI