China- Amurka

China ta yi wa Amurka gargadi kan yakin kasuwanci

Shugaban China Xi Jinping da takwaransa na Amurka, Donald Trump
Shugaban China Xi Jinping da takwaransa na Amurka, Donald Trump 路透社

Gwamnatin China ta gargadi mayar da martani ga Amurka matukar ta cutar da manufofinta na tattalin arziki, lamarin da ya haifar da fargabar yakin kasuwanci tsakanin kasashen bayan shugaba Donald Trump ya sanar da shirinsa na sanya haraji kan karafa da samfolo wato Aluminium da ake shigowa da su kasarsa.

Talla

China da ta kasance babbar kishiyar kasuwancin Amurka ta yi jinkirin mayar ta martani har zuwa jiya Lahadi, in da mai magana da yawun Majalisar Dokokinta, Zhang Yesui ya ce, China ba ta da niyar shiga yakin kasuwanci da Amurka amma muddin ta dauki matakan da ka iya illa ga maufofin kasar, to babu shakka ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen mayar da martani.

Zhang ya kara da cewa, matakan da aka dauka cikin rashin tsari za su yi illa ga huldar kasashen biyu, sannan su haddasa mummunar natijar da ba a fatan aukuwarta.

Sanarwar Trump ta sanya harajin na zuwa ne a yayin da babban mai taimaka wa shugaban China Xi Jinping ta fannin kasuwanci wato, Liu He, ya gana da hukumomin Amurka a fadar White House game da matsalolin kasuwancin kasashen biyu.

A yayin ganawar dai, bangarorin biyu sun cimma matsaya kan sasanta matsalar kasuwancin a tsakaninsu ta hanyar hada kai amma ba ta hanyar fito-na-fito ba da juna ba.

Bayan dai sanar da kudirinsa na dora harajin kashi 25 akan karafa da kuma kashi 10 akan samfolo, shugaba Trump ya nuna halin-ko-oho game da barazar mayar da martani daga sauran kasashen duniya da matakin zai shafa. Hasali ma cewa ya yi yakin kasuwanci na da kyau kuma na da saukin samun nasara akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI