Amurka

Mashawarcin Trump kan tattalin arziki ya yi murabus

Gary Cohn ya yi hannun riga da Trump kan tsarinsa na karbar harajin karafa da samfolo
Gary Cohn ya yi hannun riga da Trump kan tsarinsa na karbar harajin karafa da samfolo AP Photo/Andrew Harnik

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce, babban mashawarcin shugaba Donald Trump ta bangaren tattalin arziki, Gary Cohn na da da murabus bayan ya yi baran-baran da shugaban kan tsarinsa na kasuwanci.

Talla

Cohn da ya kasance darektan Majalisar tattalin arzikin Amurka na daya daga cikin masu adawa na cikin gida da tsarin da Trump ya bullo da shi na sanya haraji kan karafa da samfolo da ake shigowa da su kasar.

Cohn ya shafe tswon sa'oi 11 yana kokarin ganin Trump ya janye wannan tsari da ya janyo ma sa caccaka daga abokan huldar kasuwancin Amurka.

Sai dai shugaba Trump ya yi watsi da kokarin na Cohn tare da jajjada matsayinsa na fara karbar harajin nan da ‘yan kwanaki kalilan masu zuwa.

Murabus din Mr. Cohn na zuwa ne a yayin da gwamnatin Trump ke cikin hayaniya, yayin da ake ganin akwai yiwuwar wasu ma’aikatan fadar White House su ajiye aikinsu nan gaba kadan saboda rashin gamsuwa da tsare-tsaren Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI