Mutane Da Yawa Sun Kasa Numfashi A Yankin Da Ake Yaki A Syria
Wallafawa ranar:
A Kasar Syria mutane masu tarin yawa ne aka basu kulawa ta musamman da magunguna cikin gaggawa yankin Ghouta saboda matsalolin rashin iya numfashi a wuraren da ake tafka yaki wanda ya sa jami'an lafiya fargaban an yi amfani da makamai masu guba ne.
Kungiyoyin dake sa idanu akan wannan yaki na cewa mutane akalla 60 suka shiga wannan matsala a yankin garuruwan Saqba da Hammuriyeh bayan wani harin Bam da aka kai
Likitoci a wani wajen kulka da mutane da suka jikkata a Gabashin Ghouta sun ce sun baiwa mutane 29 magunguna na alamun sun shaki guba da aka watsa a inda suke.
Kungiyoyin basu bayyana an sami rasa rai ba ya zuwa yanzu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu