Isa ga babban shafi
Nepal

Akalla mutane 50 sun mutu a hadarin jirgin sama a Nepal

Jirgin da ya hatsari a Nepal tare da kashe mutane 40
Jirgin da ya hatsari a Nepal tare da kashe mutane 40 REUTERS
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Akalla mutane 40 sun rasa rayukansu, in da 23 suka jikkata bayan jirgin saman fasinjan da ke dauke da su ya yi hatsari a kusa da filin jirage na birnin Kathmandu da ke Nepal.Hukumomin kasar sun bayyana hatsarin a matsayin mafi muni da ya auku cikin shekaru a kasar.

Talla

Hukukomi a Nepal sun ce, mutane 71 ne ke cikin jirgin saman na hadin gwiwar kamfanin Amurka da Bangladesh, kuma ya yi hatsarin ne a wani filin kwallon kafa da ke kusa da filin jirage na Kathmandu bayan ya baro birnin Dhaka.

Masu aikin agaji sun babballa buraguzan jirgin da suka kone kurumus kafin samun damar zakulo fasinjojin da ke makale a cikinsa.

Kawo yanzu babu cikakken bayani game da musabbabin aukuwar hatsarin, amma wata sanarwa da hukumomi suka fitar ta ce, jirgin ya kubce wa matukinsa ne a yayin da yake dab da sauka.

Har yanzu dai ana ci gaba da ganin bakin hayaki da ya turnuke sararin samaniya a wurin da hatsarin ya auku.

Mai Magana da yawun kamfanin jirgin saman, Kamrul Islam, ya ce, 33 daga cikin fasinjojin ‘yan asalin kasar Nepal ne, yayin da 32 suka fito daga Bangladesh, sannan kuma akwai wani mutumin China guda da kuma dan asalin Maldives guda.

A yayin gabatar da jawabin jajatanwa, Firaministan Nepal, K P Sharma Oli ya yi alkawarin gudanar da binciken gaggawa kan aukuwar hatsarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.