MDD-Tarayyar Turai

Masu fama da yunwa sun haura miliyan 124 a duniya

Wasu 'yan gudun hijira a Sudan ta Kudu da ke matukar fama da matsalar yunwa sakamakon yake-yake
Wasu 'yan gudun hijira a Sudan ta Kudu da ke matukar fama da matsalar yunwa sakamakon yake-yake REUTERS/Stringer/File photo

Wani rahoton hadin-gwiwa tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai ya ce, adadin masu fama da yunwa ya haura milyan 124 a sassan duniya cikin shekarar nan. Rahoton ya ce matsalar ta ta'azzara ne a shekarar da ta gabata sakamakon yake-yaken da ake fama da su a sassan duniya.

Talla

Rahoton ya nuna cewa adadin ya karu ne da akalla kashi 15 idan aka kwatanta da na shekarar 2016 sakamakon ta’azzarar rikice-rikice musamman a yankunan da suka hada da arewa maso gabashin Najeriya da Somalia da Yemen da Sudan ta Kudu, in da ake da adadin mutane milyan 2 da ke fuskantar tsananin yunwar.

A cewar rahoton wanda bangarorin biyu bisa al’ada suka saba fitarwa kowacce shekara, matsalar ta fi tsanani a yankunan Afrika, Gabas ta tsakiya da kuma Asiya.

Kazalika rahoton ya ce, akwai yiwuwar adadin masu fama da yunwar ya karu a shekarar nan la’akari da yadda rikici ke kara tsananta a sassan duniya, yayin da za a fuskanci matsananciyar yunwa a kasashen Afghanistan da Afrika ta Tsakiya da  Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo da arewa maso gabashin Najeriya da sauran kasashen yankin tafkin Chadi da Sudan ta Kudu da kuma uwa uba Syria da Yemen da Libya.

Sai dai rahoton ya ce, har yanzu Yemen ce ja gaba a yawan mayunwata da cutukan da ke bukatar kulawar gaggawa.

Bugu da kari rahoton ya nuna cewa, akwai kuma kasashen da za su fuskanci bushewar amfanin gona da suka hada da Somalia da Ethiopia da Kenya da Senegal da Chadi da Nijar da Mali da Mauritania da kuma Bulkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.